Ranar laraba 31/8/2016 za'a rufe hada hadar saye da sayarwa na ‘yan wasan kwallon kafa na duniya a yayin da a ke daf da rufe hada hadar.
Kungiyar kwallon kafa ta Man United na shirin wani babban kamu, kungiyar tana zawarcin dan wasan gaba na Real Madrid Gareth Bale, akan kudi fan miliyan £100, inda yake yunkurin komawa matsayin sa na dan wasan da yafi kowa tsada a duniya.
Idan ba'a manta ba, a cikin watan daya gabata ne Man Utd ta sayi Paul Pogba akan kudi fan miliyan £89.
Ita kuwa Arsenal ta kammala sayen yan wasa har guda 2 wadanda suka hada da Mustafi, daga Valencia, akan kudi fan miliyan £40, sai kuma Perez, daga kungiyar Deportivo la coruna, wanda yanzu haka suke kan duba lafiyarsu kafin su fara wasa a Kungiyar ta Arsenal.
Sai kuma mai horas ‘yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Antonia Conte, ya sanya sunan Cesc Fabregas, a matsayin wanda zai sayar a bana.
Shi kuwa mai horas da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid, Zidane, ya ce yana da bukatar dan wasan nan wato James Rodriguez, ya ci gaba da kasancewa a Kungiyar ta Madrid.
Akwai yiwuwar Dan wasan kasar Ghana, mai taka leda a league ta kasar China, Asamoah Gyan, ya koma taka leda a tsohowar Kungiyar sa ta Sunderland, ta kasar Ingila a matsayin aro.