A gidansa da ke karkarar Costa Rica, masanin ilimin halitta Federico Paniagua ya haɗu da iyalansa a teburin cin abinci don gano ire-iren kwari da ya ke kiwonsu a gonar sa, kuma ya gwada dandanonsu da dankalin turawa na kwali.
Federico Paniagua wanda shine shugaban Gidan tarihi nafannin kwari da ke Jami'ar Costa Rica, shekaru uku da suka gabata ya yanke shawarar canza sanadarin gina jiki daga dabbobi da yake ci zuwa cin kwari irinsu gyare da tururuwa da kyankyasai da kuma buzuzu da sauran su - kuma yana so ya ba wasu kwarin gwiwa suma suyi haka.
"Kwari suna da daɗi," in ji shi a cikin wata hira da aka yi da shi a gonarsa mai tazarar kilomita 50 daga babban birnin San Jose.
"Za ku iya zama ku kalli wasan opera, ku kalli wasan kwallon kafa, kuyi duk wani aiki kuna cin kwari. Kuna ci daya bayan daya, a kuma kora da lemu ... za kuji kun koshi dam," in ji Paniagua.
Hukumar samar da abinci da kuma ayyukan gona ta majalisar dinkin duniya, FAO, ta fitar da kwari fiye da 1,900 iri-iri wadanda za a iya ci.
Musamman a Asiya da Afirka, ana kallon ƙananan halittun ne a matsayin abinci mai gyara jiki da ɗanɗano da ke cike da sinadaran kara lafiya, da kuma kara karfin jiki.
"Suna da dandano kamar dankalin turawa na kwali ... zaku iya cinye har faranti baki daya na irin wadannan kwari," in ji Paniagua.
Facebook Forum