A yau Talata 22 ga watan Oktobar 2019, za a dawo cigaba da fafatawa a wasannin zakarun Turai UEFA Champions League 2019/20 a matakin wasan rukuni zagaye na uku.
Kungiyoyi 32 da suka fito daga kulob daban-daban masu buga gasar lig din kwallon kafa na kasashen Turai ne suke kece raini, domin cire gwarzo a tsakanisu bisa tsarin rukuni takwas.
A yau kungiyoyi guda 16 ne zasu gwabza kamar haka, Shakhtar zata karbi bakoncin Dinamo Zagreb, sai Atletico Madrid da Bayern Leverkusen, za'ayi wasanne da misalin karfe shida saura minti biyar na yammaci, agogon Najeriya, Nijar, da Kamaru.
Da misalin karfe takwas na yammacin kuwa Club Bruges da Paris-saint German, ita kuma Galatasaray ta barje gumi da Real Madrid Olympiakos da Bayern Munich.
Sauran wasannin kuwa Tottenham a Ingila zata karbi bakoncin Red Star, sai Manchester City da Atalanta Juventus da Lokomotiv Moscow.
A yanzu haka a wannan matakin na bana cikin wasannin guda biyu, da akayi danwasan Bayern Munich Serge Gnabry, da Erling Haaland na kulob din Red Bull Salzburg, sune suka fi zurara kwallaye, wanda kwananna suka ci kwallaye hur hudu.
Facebook Forum