Wadansu jihohin sun soke wannan al’ada da kuma rage yawan jami’an da ake turawa domin kula da jin dadin masu ayyukan Ibadan.
Masu kula da lamura a harkokin ayyukan hajji sun bayyana goyon bayan daukar wannan matakin da suka ce, yana tauye ci gaban jihohin inda ake karkatar da kudaden da ya kamata a yiwa al’umma ayyukan jin dadin rayuwa kamar gina asibitai, wajen daukar nauyin aikin hajji domin siyasa abinda suka ce ba daidai bane.
Banda haka kuma, wadansu akan basu kujerun siyasar basu da halin cin yau balle na gobe, wadanda ya kamata a taimaka masu su sami abinci, yayinda wadansu kuma suke sayar da kujerun da aka basu su sami kudi.
Kamfanonin jiragen sama da suka saba jigilar alhazai sun bayyana kamala shirin jigilar alhazai kamar yadda suka saba.
Ga cikakken rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja, Najeriya.