Dr. Muhammad Ali Pate, Ministan jiha na lafiya, yayi kira ga jihohi da kananan hukumomi suyi amfani da kasonsu na SURE-P, wajen daukar nauyin wannan shirin da sauran shirye-shiryen lafiya. Duk da haka, ya nuna cewa kudin SURE-P na ‘yan Nigeria ne, Pate yace, sai wadanda ya kamata su ci moriyar shirin ne kawai za a yiwa wannan hidimar. Ya kuma gargadi shugabannin kauyuka, kungiyoyi da sauran ‘yan kasa su lura da samar da isassasun magunguna da kuma jinyar sauran cututuka.
Ya kuma bukace su, su kai rahoton rashin adalci ga hukumomin da ya kamata. Bisa ga cewarshi, ta haka ne za a tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Dr. Pate ya bayyana cewa, kimanin mata miliyan daya suka je awon ciki a asibitan gwamnati bara, abinda ya sa aka ceci rayuka 218,000.
A nashi bangaren, directa hukumar lafiya matakin farko, Dr. Ado Muhammad, ya bayyana cewa, an biya kowacce mace daga cikin matan da suka fara amfani da wannan shirin N1,000 daga wata daya na farko zuwa uku, kana kuma za a biya su domin kai yaransu a yi amsu allurar rigakafi. Bayan sun haihu kuma aka ba, matan N2, 000 kowacce, abinda ya kai adadin kudin da aka ba kowacce mace N5, 000. Ya kara cewa, tunda aka fara yin shirin a Kuja, an sami Karin mata dake zuwa asibiti na gwamnati sosai.
An kuma fara buga wata jarida mai suna “MAMA” domin yiwa mata masu ciki bayani kan kula da lafiyarsu.