WASHINGTON, DC —
Tawagar Gwamnatin Najeriya ta ziyarci Bauchi, domin mika sakon ta’aziy, da kuma jajantawa mutanen da suka rasa dukiyoyinsu a sanadiyar fashewar bom, da ya fashe a kasuwar central Market, a ranar 22, ga w2annan watan.
Tawagaar da Ministan Babban birnin tarayya Abuja, Bala Muhammad Kauran Bauhi, kewa jagoranci, ta zuyarci kasuwar da asibiti, ta kuma kai ziyarar ban girma ga fadar mai martaba sarkin Bauchi, Rilwanu Sulaiman Adamu.
A jawabisa Ministan na Abuja, yace makasudin zuwan tawagar shine domin yin ta’aziya, a madadin shugaban kasa da kuma Gwamnatin tarayya, ga ‘yan kasuwa da kuma jama’ar jihar Bauchi domin tashin bom din da ya faru a kusuwar Bauchi.