Wannan matakin na zuwa biyo bayan tankade da rairayar da gwamnatin ta kaddamar don gano malaman bogi wanda ya yi sanadin rashin biyan mutane su dari hudu da casa'in da bakwai Inji daya daga cikin wadanda abin ya shafa Malam. Mahi Umar wanda ya ce duk da kin biyansu hakkokinsu suna zuwa aiki.
Shugaban kungiyar malaman na kasa reshen karamar hukumar Donga Komred Danladi Ibrahim ya shaidawa Muryar Amurka cewa ba su da zabi illa su kai kokensu gaban Allah ganin kwalliya ba ta mai da kudin sabulu ba duk da daukar dukkan matakan da suka halartar.
Shi ma shugaban kungiyar reshen jihar Taraba Komred Aliyu Tafida ya yace sun bukaci gwamnatin ta sake tantance wadanda aka tsaida albashinsu amma zahiri har yanzu bata basu wata amsa takamaimiya ba.
Da yake kare matsayin gwamnatin jihar Taraba, shugaban hukumar kula da makarantu firamare Mal. Yakubu Saleh yace tankaden ya bankado malaman bogi dubu daya da dari bakwai kuma gwamnati na fatar da zarar an kammala tankade da rairayar zata maido da kudade da za a karkata wajen yi wa jama'a hidima.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.