Dukiya na miliyoyin naira ne suka salwanta musamman amfanin gona a wasu yankuna na Mambillan, sanadiyar ambaliyar ruwa, saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Al’ummomin da lamarin ya shafa sun hada da na Yurum,Mbaso, Yana da Njeke dake cikin karamar hukumar Sardauna inda aka kai musu wannan tallafi na abinci da suka hada da buhunan masara dari biyu.
Alh, Abubakar Zubairu Kabri, hadimin gwamnan jihar, shine ya wakilci gwamnan jihar wajen bada buhunan hatsin.
Mai martaba Lamidon Kuma Alhaji Adamu Gambo Nimeso da shugaban karamar hukumar Sardauna Reverend Goodwill Sol sun nuna farin cikinsu da wannan tallafin da gwamnatin jihar ta turo.
Matsalar ambaliyar ruwa na neman zama ruwan dare a Najeriya, wanda kuma alkalumman hukumomin bada agaji a kasar ke cewa fiye da mutum dari sun mutu ta sanadiyar ambaliyar baya ga hasarar dukiya. Wannan al’amari ya faru ne yayin da aka soma sako ruwa daga madatsar ruwan Lagdo na kasar Kamaru dake makwabtaka da jihohin Taraba da Adamawa.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz
Facebook Forum