Manyan malaman da gwamnatin Osun ta kai kara sun hada da malaman makarantar kimiya da fasaha dake garin Ire da kwalajojin ilimi dake Ilesha da Ilaro da kuma makarantar kere-kere dake Esa Oke
Lauya Wale Afolabi shi ya wakilci gwamnatin jihar a kotun. Yace a karkashin doka kafin ma'aikata su ce suna da kungiya dole ne su yi rajista da ma'aikatar ayyuka ta tarayya. Wadanda suke kiran kansu kungiyar malaman manyan makarantu na jihar Osun basu yi rajista ba kamar yadda doka ta tanada. Sabili da haka basu da izinin kiran kansu kungiya har ma su yi yajin aiki.
Lauya Afolabi yace tuni suka rubutawa ma'aikatar aiki ta tarayya domin su sami tabbacin cewa kungiyar manyan malaman ta halal ce bata sabawa doka ba.
Da suke mayarda martani game da karar malaman ta bakin kakakinsu Dr Shola Ojeniyi bayan sun kammala taronsu a garin Ire sun ce lamarin abun takaici ne domin sun dade suna tattaunawa da gwamnati amma kwaram sai ta kaisu kara.
Dr Ojeniyi yace gwamnatin jihar Osun da ta dade tana muamala da kungiyarsu yanzu ta ce bata bisa doka. Sun dade suna yin yarjejeniya amma haka kawai gwamnatin ta ce bata yi dasu kuma.
Za'a fara shari'ar mako mai zuwa kuma malaman sun ce suna shirye.
Ga karin bayani.
`