A taron da kwamitin kare wuraren Ibada na duniya ya gabatar a Abuja, gwamnatin kasar Norway ta tsara yadda za'a kare wuraren ibada a duniya
Tayi misali da birnin Jerusalem ko Qudus da cewa wani birni ne na musamman dake da wurare masu tsarki da dama da suke da mahimmanci ga duka addinai da suka samo asali daga Annabi Ibrahim.
Inji daraktar kwamitin akwai matukar bukata a kare wuraren lamarin da tace aiki ne na kowa da kowa. Burinsu ne su tabbatar da wuraren ibada a duk fadin duniya ciki har da birnin Qudus an karesu.
Wazirin Katsina Alhaji Sani Abubakar Lugga yana cikin manyan baki da suka gabatar da jawabi. Yace shugabannin addinai su san cewa kowa ya dauki addinansa da mahimmanci saboda haka a ilimantu a san cewa addinai nada mahimmanci. Yakamata a girmamasu, a tsaresu a kuma fahimcesu domin kawo zaman lafiya. Muddin babu zaman lafiya kare wuraren addini ba zai yiwu ba. Kare wuraren addini ba tare da kare masu addinin ba tamkar yin shuka ne ba tare da rufe abun da aka shuka ba.
Wadanda suka shirya taron sun bada misali da rikice-rikicen da ya faru a jihar Filato. Malam Sani Mudi shi ne mai taimakawa gwamnan jihar Filato akan harkokin addini yace abun da gwamnanti ta sa gaba shi ne a tabbatar da zaman lafiya mai dawama. Yace gwamnati zata yi duk abun da ya kamata ta tabbatar zaman lafiya ya dore a jihar. Yanzu tana tattaunawa da kungiyoyi kamar na addini da shugabannin al'ummomi da zummar warware duk matsalolin dake haddasa rashin zaman lafiya.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum