Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta sa-ido akan ayyukan kafafen sada zumunta na yanar gizo, wanda ta ce a yau kafafen yanar gizo na cin karensu ba babbaka. Don haka gwamnati za ta dinga duba yadda suke gudanar da ayyukansu.
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya bayyana hakan a yau Talata, ya kuma kara da cewar gwamnati zata fito da tsare-tsare da zasu kawo tsafta a kafofin sadarwan. “Kafafen sadarwar zamani na yanar gizo na haddasa haddura ga rayuwar jama’ar kasar.”
Najeriya ba ita ce kasa ta farko ba da ta fara bibiyar irin wadannan ayyuka da kakafen na sadarwa ke yi ba, akasarin abubuwan da ke shiga kafafen abubuwan ban mamaki, da ban dari ne a wasu lokutan. Don haka zamu samar da tsari da zai tabbatar da babu wasu abubuwan cin zarafi ga wasu da ake sakawa a kafofin.
Facebook Forum