Ta fara shirin ne a jihohin Oyo da Osun. Shirin mai lakabin mayarda da gani ga wadanda suke da matsalar idanu na Goodluck Jonathan za'a yi kwanaki biyar a na gudanarwa.
Mai shugabancin shirin Uwargida Abolanle Oyegoke ta ce an tsara shirin ne domin taimakawa 'yan Najeriya masu fama da matsalolin idanu. Dr Funke Ajoloko tana daya daga cikin likitoci masu gyaran idanun. Ta ce wasu masu gyaran idanu na gargajiya suna jawo matsala yayin da suke anfani da tsinke su soke wajen dake gani a cikin ido musamman idan cutar yanar ido ce. Yin hakan yana yiwa ido la'ani ya kuma lalace har ya kaiga makanta. Sabili da haka ta bukaci wadanda suk da matsala da idanunsu su guji yin anfani da maganin gargajiya.
Wasu da aka yiwa gyaran idanu sun bayyana ra'ayoyinsu. Sun roki gwamnati ta kara
kwanakin yin gyaran idanun saboda yawan jama'a. Wata ta ce lokacin da ta ga bata iya karatu sosai da ta ji batun gyaran idanu shi ya sa ta kawo kanta. Sabili da haka ta godewa shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ana zaton za'a cigaba da gyaran idanu kyauta da bayar da magunguna zuwa sassan yankunan Najeriya.
Ga karin bayani