Hajiya Kudirat Abiola ita ce uwargidan Chief M.K.O.Abiola hamshakin attajiri wanda kuma aka kyautata zaton shi ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1992 a karkashin jam'iyyar SDP.
A wani takaitacen zama da kotun kolin Najeriya tayi jiya Alhamis ta ba gwamnatin Legas izinin daukaka kara akan sako Manjo Hamza Al-Mustapha da aka yi shekaru uku da rabi da suka wuce.
Oluwayemisi Osunsanya wadda ta wakilci gwamnatin Legas a zaman kotun kolin tace sun yi murna an basu izinin daukaka kara. Tace zasu yi aikin kawo shaidu bisa lokaci.
Shi ma Joseph Daudu lauyan Manjo Hamza Al-Mustapha yace sun ki a ba gwamnatin Legas damar da ta nema amma kotun kolin ta basu. Yanzu gwamnatin Legas nada damar daukaka kara cikin kwanaki talatin daga jiya Alhamis.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.