Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Legas Ta Musanta Barkewar Cutar Sankarau a Jihar


Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode
Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode

Kwamishanan jihar Legas Dr Jide Idris shi ya musanta labarin da ke cewa an samu bullar cutar sankarau a jihar wai har wasu mutane biyu sun rasu.

Hukumar dake kula da cututtuka masu yaduwa ta gwamnatin tarayya ita ce tace an samu barkewar cutar sankarau a jihar ta Legas.

Dr Jide Idris a taron da yayi da manema labarai yace babu kanshin gaskiya a labarin barkewar cutar a jihar kuma kawo yanzu babu alamar cutar a jihar. Amma yace ko shakka babu an samu barkewar cututtuka dake da nasaba da cutar sankarau musamman a arewacin Najeriya. To saidai a jihar Legas babu wani rahoton bazuwar cutar musamman sankarau irin na C mai kisa nan da nan.

Dr Jide Idris yace akwai cutar sankarau iri biyu. Akwai mai zafin akwai kuma wadda bata da zafi. Yace akwai wadda bata da hatsari kuma ana samunta a wasu jihohi amma ba irin na arewacin Najeriya ba.

Dangane da matakan da gwamnatin jihar ke dauka domin hana bullar cutar a jihar, Dr Jide Idris yace akwai jami'an kiwon lafiya da suka saba fadakar da al'umma game da yadda zasu kula da lafiyarsu. Jami'an suna zagaya koina cikin duka kananan hukumomin jihar domin fadakar da al'umma su kasance cikin shiri da daukan matakan rigakafi.

Garahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG