Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin jihar Bauchi ta bankado ma'aikatan bogi


Kwamitin bincikar kayan da wasu suka mallaka ba kan kaida ba ya bankado ma'aikatan bogi fiye da dubu talatin da suke amsar kudin gwamnati kimamin nera biliyan daya da miliyan dari uku ko N1.3b

Shugaban kwamitin kwato kayan gwamnati daga hannun mutanen da suka mallakesu ba kan ka'ida ba Air Commodre Ahmed Tijjani Baba Gamawa mai ritaya shi ya shaidawa manema labarai.

Yace sun samu ma'aikata na bogi da suka fi mutane dubu talatin. Dangane da kudaden da suka binciko na mutanen sun dara N1.3b. Yace idan Allah ya yadda zasu kaiga manufa. Duk wadanda suka da hannu a cikin lamarin za'a gurfanar dasu gaban shari'a.

Amma inji Alhaji Muazu Shira mai sharhi akan alamuran yau da kullum yace ba daidai ba ne a yanzu gwamnati tace ta samu ma'aikatan bogi ganin cewa dubban ma'aikatan jihar basu karbi albashinsu ba. Yace akwai dubban mutane da basu sami sabuwar lambar asusu ko BVN ba. Kamata ya yi gwamnati ta bari sai an kammala duk ayyukan da aka dibar ma wa'adin watanni biyu kafin tace ta samu ma'aikatan bogi. Duk mutanen dake karbar albashi a bankunan karkara basu samu albashinsu ba tukunna.\

Ta bakin kakakin jam'iyyar APC a jihar Alhaji Aliyu Zalla yace akwai mudin da za'a biya ma'aikata muddun a tantancesu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG