Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jigawa Ta Bankado Ma’aikatan Bogi 6, 348

Ma'aikata sun kasance a rufe A Abuja
Ma'aikata sun kasance a rufe A Abuja

Ya kara da cewar rahoton aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan da aka gudanar a fadin jihar, ya nuna cewa an gano ma’aikatan bogi 6, 348 tare da alkintawa jihar Naira miliyan 314 a kowane wata.

Gwamnatin Jigawa ta bayyana cewa ta bankado ma’aikatan bogi 6, 348 yayin aikin tantance ma’aikatanta daya gudana a jihar.

Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Sagir Musa ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar yau Talata a birnin Dutse.

Ya kara da cewar rahoton aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan da aka gudanar a fadin jihar, ya nuna cewa an gano ma’aikatan bogi 6, 348 tare da alkintawa jihar Naira miliyan 314 a kowane wata.

A cewar Sagir Musa, majalisar zartarwar jihar ta yi nazarin rahoton tare da kafa cibiyar cigaba da daukar bayanan ma’aikata a ofishin shugaban ma’aikatan jihar.

Ya ce, hakan zai hanzarta kammala aikin daukar bayanai da tantance ma’aikatan da ake yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG