Gwamnatin jahar Kaduna ta sassauta dokar hana fita wadda ta kafa sanadiyyar mummunan tashin hankalin nan da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Sassauta dokar ya biyo bayan taron da aka yi na kwamitin tsaron jahar inda aka yi la’akari da bukatar barin mutane su yi walwala matukar ba a take doka da oda ba. To amma ba ko ina aka sassauta dokar ba. Har yanzu dokar ta hana fita ta sa’o’i ashirin da hudu ta na aiki a wasu unguwanni kamar biyar haka, wadanda su ka hada da Kabala West, da Sabon Tasha da Kabala Doki da Narayi da Marabar Rido.
Daraktan Yada Labarai na gwamnatin jahar Kaduna, Mr. Samuel Aruwan, ya ce an yanke shawarar cigaba da aiwatar da dokar a wasu wararen ne saboda wasu rahotannin da ke nuna cewa akwai barazana ga tsaron lafiya da kuma dukiyoyin jama’a. Ya ce hatta wasu unguwannan da aka sassauta masu dokar hana fitar, an dan bandanta tsawon dokar bisa ga yanayin da ake ciki a wuraren.
Tuni dai mazauna Kaduna su ka fara bayyana ra’ayoyinsu game da dake dokar da ma yanayin tsaro da kuma zamantakewar al’ummar jahar da ma kasar bakoi daya. Kwamred Hassan Haruna Aliyu na Kasuwar Shirkh Mahmud Gummi ya bayyana farin cikinsa da sassauta dokar. Haka zalika, wata malama Zainabu ta ce dagewar za ta taimaka gaya wajen samun abin masarufi da kuma walwala .
Ga dai wakilinmu a Kaduna Nasiru Yakubu da cikakken rahoton :
Facebook Forum