Wani shirin gina babban coci na kasa kan dala miliyan 400 ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar Ghana, Sabon shugaban kasa, John Dramani Mahama, ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan wannan shiri da tsohon shugaban kasa Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya kaddamar. Wannan ya biyo bayan matsin lambar jama’a da ke fuskantar kalubalen tattalin arziki mai tsanani.”
Tsohon shugaban kasa Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya yi shelar shirin gina babban cocin (wato Cathedral) a shekarar 2017, alkawarin da ya yi a matsayin sadaukarwa ga Allah saboda nasararsa a zaben 2016. Saidai kawo yanzu, kimanin dala miliyan 58 daga kudaden gwamnati wanda aka kashe yayin fara gina Cathedral din ya haifar da cece-kuce, inda gwamnatin da ta ke dab da karbar mulki ta kafa kwamitin bincike a kai.
Wasu mabiya addinin Kirista, na ganin gina babban cocin ya na da mahimmanci, wasu kuma na ganin ba shi da muhimmanci, kamar yadda babban Pastor Flex Nze ya bayyana cewa, bai da ra'ayin a gina coci alhalin jama'ar kasa na cikin halin yunwa.
Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama, ya ce ya kamata a gudanar da bincike don gano yadda aka kashe kudaden jama’a wajen gina wannan babban coci.
Shi kuwa Jafaru Dan Kwabiya kwararre a fannin tattalin arziki, ya ce, yin amfani da kudaden gwamnati a kan wani aiki mai tsadar gaske irin wannan a lokacin da jama’a ke fama da matsin rayuwa, ba abu ne mai kyau ba. Ya kamata ace an karkatar da wadannan kudade zuwa magance matsalar wutar lantarki, abinci a makarantu da dai sauran su.
A yanzu dai, mafi yawancin jama'ar kasa suna farin ciki da wannan bincike kan batun gina babban cocin kasa wato Cathedral wanda zai lakume dala miliyan 400 wajen gina shi da shugaban kasa John Dramani Mahama ya fara.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Abdulkarim:
Dandalin Mu Tattauna