Gwamnatin Borno ta gudanar da wannan aikin tantance tsarin biyan ma’aikatan ne a cikin wata guda ta kuma gano wasu ma’aikata masu karancin shekaru da kuma wadanda shekarun su ya haura na aiki a cikin kananan hukumomi 19 na jihar mai kananan hukumomi 27.
Kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu a jihar Borno Bele ya ce an sami rarar sama da miliyan 57 tsakanin ma’aikatan da shekarun su ya haura 60, kana aka sami rarar sama da Naira miliyan 93 tsakanin wasu da suka karbi takardun tantancewa amma kuma basu bayyana gaban kwamitin ba, wanda hakan ke tabbatar da dukkanin su ma’aikatan bogi ne.
Shugaban Ma’aikatan kananan hukumomi Mallam Mustpha Bulama ya ce akwai kuskure da a kididdiga da gwamnati bayar, ya kuma ce gwamnatin kan ta ta tabbatar da haka. Ya ce su ma ma’aikatan ba su ra’ayin a kyale mutane da shekarun su ya kai 60 su ci gaba da aiki saboda yara da ke tasowa.
Sai dai ya yi kira ga gwamnati cewa idan ma’aikata suka ga wata matsala da ke bukatar gyara, ya kamata gwamnati ta ba da himma wurin yin wannan gyara.
Gwamnatin Borno yanzu haka ta lashin takobin ci gaba da wannan aiki na tantance wadannan ma’aikatan kananan hukumomin, musamman a cikin sauran kananan hukumomi guda takwas da suka saura.
Ga dai rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
Facebook Forum