Shugaban kwamitin labaru na majalisar wakilan Najeriya Abdulrazak Namdas, ya ce majalisar za ta dauki matakai don kaucewa shirin Amurka na sanya kafar wando daya, da kasashen da mutanen su kan shantake bayan karewar izinin zaman su na gajeren zango.
Namdas a zantawa da Muryar Amurka, na magana ne kan shirin gwamnatin shugaba Donald Trump, na daukar matakai masu tsauri wajen ba da “VISA” ga ‘yan kasashen da jama’ar su kan shantake a Amurka bayan karewar izinin.
Cikin kasashen da matakin na Fadar WHITE HOUSE zai shafa, akwai kasashen Afurka 5 da su ka hada da Najeriya, Chadi, Saliyo, Eritrea da Laberiya.
Matakan da Amurka ke shirin dauka sun hada da takaita izinin zaman ko tsaurara samun izinin, da kuma daukar karin matakan zafafa hanyar samun “VISA” ta dalibai da masu zuba jari.
Majalisar wakilan Najeriya, inji Namdas za ta bi matakan wayar da kan masu shiga Amurka daga Najeriya don mutunta ka’idar izinin shiga kasar, don gudun kar hakan ya jawo rudanin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Namdas na da ra’ayin cewa mutuncin ‘yan Najeriya ya farfado karkashin gwamnatin shugaba Buhari.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum