Wani mai magana da yawun gwamnatin Afghanistan ya ce mutane 43 ne suka mutu, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani ginin gwamnati da ke birnin Kabul a ranar Litinin.
An kai harin da yamma, lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa wata mota da ke makare da bom a bakin ginin, wanda ke dauke da ma’aikatun gwamnati da dama, da suka hada da ma’aikatar masu nakasa da ta tsofaffin sojoji.
Bayan da ya fasa kofar shiga ginin, dan bindigar ya ruga cikin ginin inda ya kwashe tsawon sa’o’i bakwai yana musayar wuta da ‘yan sanda.
Mai magana da yawun ministan lafiya, Waheed Majro, ya ce akalla mutane 10 sun ji rauni a harin. Sannan dan sanda daya da mahara 3 sun mutu a lokacin wannan harin.
Jami’ai sun ce ma’aikata sama da 200 aka kubutar bayan faruwar hare-haren. Har ila yau, akwai wasu muhimman gine-gine da ma’aikatu a wannan unguwa da aka kai harin, wacce ke gabashin birnin na Kabul.
Facebook Forum