Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Lalata Baburan Hawa 1500 a Jihar Legas


Baburan da aka kwace
Baburan da aka kwace

Gwamnatin jihar Legas ta sake lalata baburan hawa guda 1,500 da jami’anta suka kwace daga hannun mutanen dake hawansu a kananan hukumomi guda 10 da yankuna 15 da aka haramta amfani da su.

Kananan hukumomin da yankunan da abin ya shafa sun hada da Kosofe, Oshodi-Isolo, Somolu, Mushin, Apapa, Ikeja, Lagos Island, Lagos Mainland, Surulere, da Eti-Osa.

Kwamishinan sufurin jihar Oluwaseun Osiyemi ya jagoranci lalata baburan a ofishin hukumar dake kula da sufurin a unguwar Alausa, inda ya sake jaddada matsayin gwamnatin Lagos na ci gaba da hana amfani da baburan da kuma hukunta duk wanda aka samu yana zirga zirga da su a yankunan da aka haramta.

Babura da aka kwace
Babura da aka kwace

Osiyemi yace jami’an gwamnati zasu ci gaba da farautar masu bijirewa dokokin gwamnati wajen amfani da baburan, yayin da hukuncin daurin shekaru 3 ke kan duk wanda aka samu da laifi, baya ga murkushe baburan.

Kwamishinan yace an dauki matakin haramta amfani da baburan a manyan titunan jihar ne domin tabbatar da doka da oda da kuma rage haduran da ake samu na ababan hawa.

Osiyemi ya gargadi mazauna birnin Legas cewar su kaucewa amfani da baburan a matsayin hanyoyin sufuri saboda hadarin dake tattare da su.

Yan babura a kasuwa
Yan babura a kasuwa

Legas dai ita ce cibiyar tattalin arzikin Najeriya kuma za a iya cewa ita ce jiha mai mafi yawan jama'a a kasar. Amma kuma jihar ta na da wasu matsalolinta daban-daban kamar cunkoson ababen hawa da kuma karancin hanyoyin sufurin jama'a.

Sakamakon haka dubban masu babura kan bazu kan tituna don kasuwanci, tare da cike gibin da ke tattare da zirga-zirgar jama'a da kuma samun kudin shiga na kansu.

Sai dai gwamnatin jihar ta hanyar dokar zirga-zirgar ababen hawa ta Legas 2012 (wanda aka sabunta a shekarar 2018), ta haramta gudanar da ayyukansu a cikin biranen jihar, tare da kafa kwamitin da zai sanya ido tare da tabbatar da dokar, saboda rashin bin ka’ida da hadurran da ba a saba gani ba.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2021, Sakateriyar Alausa da ke Ikeja, karkashin gwamnatin jihar Legas ta murkushe dimbin babura da aka kama a wurare daban-daban a Legas sakamakon karya dokokin hanya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG