Gwamnan Jihar Dr Musa Rabiu Kwankwaso ya mayarda martani game da lamarin. Ya ce suna da labari cewa an bada umurni daga sama cewa a zo a kwashe duk shugabannin majalisar jihar. An kamasu domin a hana su yin aikin su da tsarin mulki ya basu dama su yi. Ya ce an tafi da su zuwa Abuja domin a ci mutuncinsu kuma aci mutunci jihar Kano gabaki daya.
Gwamna Kwankwaso ya cigaba da cewa yana da labari sun shiga jam'iyyar APC reshen jihar Kano. Ya ce abun takaici ne a ce gwamnati ta zama mai yin karan tsaye tana mulkin kama karya. Ya ce suna bakin ciki da ita hukumar EFCC da ta bari ana anfani da ita a matsayin karen farauta.
Jiya Litinin ne hukumar EFCC ta kama shugaban majalisar da mataimakinsa da wasu tara ta tafi dasu Abuja. A cikin wasikar sanmacin da Ishaq Salihu jami'ain hulda na hukumar a jihar Kano da sama hannu ba'a bada dalilan kama 'yan majalisar ba. To sai dai masu kula da harkokin yau da kullum sun ce kamasun kila yana da nasaba da kasafin kudin shekara mai zuwa da gwamnan jihar ya mikawa majalisar wanda yake kunshe da kudi fiye da nera miliyan dubu ashirin da takwas.
Mahmud Ibrahim Kwari nada cikakken bayani.