Gwamnan Jahar Naija Alhaji Abubakar Sani ya ce muddun manyan motocin tirela su ka cigaba da bin kan hanyoyin kasar nan to kamai gyara su da aka yi, kuma ko da nawa aka kashe kansu su za su yi ta lalacewa ne kawai.
Da aka tambaye shi matakin da zai dauka a jaharsa game da batun kalacewar hanyoyin, sai ya ce ba shi da hurumin cewa komai game da hanyoyin gwamnatin tarayya duk da yake a jaharsa hanyoyin su ke. Ya ce da a ce motocin tirela na daukar matsakaitan kaya da hanyoyin bas u lalace haka ba.
Gwamna Sani ya ce ya yi magana da Mukaddashin Shugaban Kasa da kuma Ministan da abin ya shafa kuma sun yadda cewa abin da na fada gaskiya ne saboda idan ba mu dau matakin da ya dace ba za mu yi ta kashe kudi mai yawa ne kawai a banza.
Ga babi na farko na hirar da Ladan Ayawa ya yi da gwamnan na Naija:
Facebook Forum