Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jahar Bauchi Ya Sha Alwashin Sulhunta Sarki Sanusi Da Gwamna Ganduje


Gwamna Abdulkadir Bala Mohammed Duguri
Gwamna Abdulkadir Bala Mohammed Duguri

A cigaba da nemar maslaha game da takaddamar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi (ii) da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Kauran Bauchi, Gwamna Abdulkadir Bala Mohammed Duguri, ya lashi takobin ganin takaddamar ta kawo karshe.

Gwamnan jahar Bauchi, Abdulkadir Bala Muhammed Kauran Bauchi, ya kuduri aniyar ganin an kawo daidaito a rikicin da ya faru tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.

Kauran Bauchin ya yi wannan furucin ne a fadar gwamnatin jahar Bauchi, a lokacin da tawagar da sarkin Kano ya tura bisa jagorancin Makaman Kano, Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim, domin Kai ziyarar taya shi murnar nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Bauchi.

A jawabinsa, gwamnan jahar Bauchi Abdulkadir Bala Muhammed Kauran Bauchi, ya bayyana takaicinsa dangane da yanayin da masarautar Kano ta samu kanta ciki, ya ce Kano ita ce abin misali ga dukkan bahaushe da kuma arewacin Najeriya, sabili da haka wargaza ta babbar gobara ce da ya kamata a kasheta.

Tunda farko kuwa, jagoran tawagar, Makaman Kano Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim, ya fayyace wa gwamnan makasudin kawo ziyarar da mai martaba Sarkin Kano Muhammadau Sunusi na biyu ya umurce su da su kawo.

A gefe guda kuma, gwamnan jihar Bauchin ya kai mubaya’a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin fayyace masa yadda abubuwa ke gudana a jahar Bauchi a siyasance.

Ga Rahoton Abdulwahab Muhammed Cikin Sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG