Koriya ta arewa ta sake harba wani makami mai linzame, abin da ke nuni da cewa ta saba alkawarin da ta yiwa shugaban Amurka Donald Trump na kaucewa gwajin makamai bayan da suka cimma matsaya akan babban atisayen hadin guywar sojojin Amurka da na koriya ta kudu.
Ko daya ke, Trump ya ce bai dauki gwajin makamin da koriya ta arewa ta yi a matsayin saba alkawari ba. Kafin ya tashi daga birnin Washington zuwa taron kolin G-7 da za a fara yau a Faransa, shugaban na Amurka ya ce shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un baya boye mashi wani abu. Ya kuma ce, Kim na son gwajin makamai masu linzame, amma a yarjejeniyar da suka cimma basu hana gwajin harba makamai masu cin gajeren zango ba.
Gwamnatin Japan ce ta sanar da harba makamin da safiyar yau Asabar. ‘Yan mintoci daga baya kuma rundunar sojan koriya ta kudu ta tabbatar da gwajin makamin, ta na mai cewa Koriya ta arewa ta harba makami daga kudancin yankin Hamgyong zuwa gabashin gabar tekun ta.
Facebook Forum