Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GRACE ALHERI ABDU: Domin Iyali- Taron Shawo Kan Matsalar Satar Kananan Yara, Nuwamba, 14, 2019


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A ci gaba da nazarin hanyoyin shawo kan sace al'umma da kare hakkokin bil'adama, yau shirin Domin Iyali ya yada zango a birnin tarayya Abuja inda Sashen Hausa ya hada kan masu ruwa da tsaki domin neman hanyar shawo kan sace sacen kananan yara biyo bayan kwato wadansu kananan yara tara da aka sace a birnin Kano aka kai Anambra inda aka canza masu sunaye da addini.

Taron ya sami halartar jami'an 'yan sanda, shugabannin addinai, kungiyoyi masu zaman kansu, 'yan gwaggwarmaya da sauran masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen Abuja.

Saurari kashin farko na tattaunawar.

Tattaunawa kan satar yara-PT1-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:15 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG