Da saukan shugaban a filin jirgin saman Sultan Abubakar III ya zarce zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi. A jawabinsa yace ziyarsa bata da nasaba da siyasa duk da cewa yana tare da shugabannin jam'iyyarsa da ma tsohon gwamnan jihar Alhaji Attahiru Baffarawa wanda kwana kwanan nan ya canza sheka zuwa PDP.
Shugaba Jonathan yace basu zo domin wata manufar siyasa ba, sun zo ne domin Sarkin Musulmi na cikin daya daga manyan shugabannin kasar da suke fafitikar hadin kan kasar da kuma cigabanta. Yace sabili da haka ne duk lokacin da suka samu dama sukan ziyarci Sarkin domin fahimta da shawarwari dangane da makasudin cingabar kasar.
Gwamnan jihar Sokoto Magatakarda Wamako wanda ya tarbi shugaban ya kuma rakashi fadar Sarkin Musulmi ya soki ziyarar shugaban bayan shugaban ya tafi a wani taron 'yan jarida da ya kira. Yace ziyarar ta siyasa ce amma ya bata wata suna daban. Yace mutum ne kasa na cikin matsala amma kullum yana yawon siyasa da yin shagulgula. Yace bai kula da irin jihar Adamawa ba inda ake kashe mutane. Kamata yayi ya ziyarci irin wadannan jihohin dake samun hare-hare. Yakamata ya je yayi masu jaje. Shugaban bai san darajar rayuwan 'yan Najeriya ba.
Ga karin bayani.