Kimanin manyan kwararru a fannin binciken kwakwa kan cutar AIDS dubu 25 ne daga kasashen duniya, da shugabannin addini da jami’an diplomasiya da kuma masu ruwa da tsaki zasu fara wani taron kasa da kasa kan yaki da cutar kanjamau gobe Lahadi.
Za a yi toron da ake gudanarwa bayan kowacce shekara biyu daga ranar 22 ga watan Yuli zuwa 27 a birnin Washington, birnin da ya kasance daya daga cikin biranen da aka fi yawan masu dauke da kwayar cutar kanjamau a Amurka.
Sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton, da maidakin tsohon shugaban kasar Amurka Laura Bush zasu yi jawabai a wurin taron. Sauran manyan jami’an da zasu yi jawabai sun hada da shugaban babban bankin duniya Jim Yong Kim, da shugaban kamfanin komfuta na Microsoft kuma fitaccen mai halin jinkai Bill Gates.
Kanjamau cuta ce dake karya garkuwar jiki, ta sa mutane su kamu da cuta cikin sauri.
Ana samun kwayar cutar kanjamau a ruwan jikin mutum dake dauke da cutar kuma aka daukarta ta wajen dagula jinin mai dauke da cutar, kojkima’I, ko kuma daga uwa zuwa jariri lokacin da mace take da ciki, ko shayar da jariri da nono.
Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane miliyan 34 ne ke dauke da kwayar cutar HIV a duniya, yayinda kimanin miliyan daya da dubu dari bakwai suka mutu ta dalilin cutar a shekara ta dubu biyu da goma sha daya.
Jiya Jumma’a babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya zabi Micheal Kazatchkine a matsayin manzonshi na musamman kan cutar kanjamau a gabashin kasashen turai da tsakiyar Asiya inda cutar take ci gaba da yaduwa.
Makon jiya Mr. Ban ya zabi tsohuwar mataimakiyar babban magatakardar Majalisar Dinkin duniya Asha-Rose Migiro a matsayin manzo ta musamman kan cutar kanjamau a Afrika, nahiyar da tafi kowacce yawan masu dauke da kwayar cutar HIV a duniya.