Wata mummunar gobara data tashi cikin motar bas ta hallaka mutane 4, ciki harda yara 3, a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.
Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin Asabar din data gabata sa’ilin da wata motar bas kirar Hummer dauke da fasinjoji 44 ta kama da wuta a kusa da kwalejin ‘yan mata ta hadaka.
A cewar rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, gobarar ta tashi ne bayan da wata katifa dake daure a bayan motar ta taba salansa, abinda ya sabbaba tashin mummunan tashin wuta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Sp Lawan Shisu, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda yace gobarar ta tashi ne bayan da katifa ta kama da wuta daga salansar motar.
An yi rashin sa’a, gobarar ta hallaka mutane 4, ciki harda wata mata mai shekaru 40 da kananan yara 3 masu shekaru 5 da 3 da kuma 10 wadanda suka kone kurmus.”
Dandalin Mu Tattauna