Tun a shekarar da ta gabata aka fara batun cewa jam'iyyar NPP ya dace ta tsayar da mataimakin shugaban kasa Dakta Mahamudu Bawumia da tsohon ministan cinikayya da masana'antu Alan Kyeremanten a matsayin abokan takara a babban zaben kasa mai zuwa.
Wasu jiga-jigan jam'iyyar NPP kamar tsohon shugaban jam'iyyar Freddie Blay, da tsohon Minista kuma daraktan sadarwa Nana Akomea, da mamban majalisar dattijai na jam'iyyar, Hackman Owusu Agyeman, da shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki na kasa Osei Kyei Mensah Bonsu, ne suka bayyana wa kafofin yada labarai dabam-daban ra'ayinsu kan cewa idan aka hada Dakta Mahamudu Bawumia da Alan Kyeremanten a matsayin abokan takara, za a kara hada kan jam'iyyar kuma hakan zai taimaka wajen samun nasara a zaben 2024.
Dakta Bawumia ya kasance mataimakin shugaban kasa tun daga shekarar 2017 shi kuma Mista Alan Kyerematen ya yi takara da shugaba Akufo-Addo har sau uku kafin Akufo ya lashe zaben 2016. 'Yan takarar biyu da suka fito daga kudu da arewacin kasar sun cika sharuddan shugabancin jam’iyyar.
Sadat Hamisu Barko, jami'in sadarwa ne na jam'iyyar NPP, yace, idan 'yan takarar suka amince a hada su abokan takara lallai hakan zai kawo hadin kai a jam'iyyar kuma lashe zaben 2024 zai yi musu sauki.
Amma shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki Osei Kyei Mensah Bonsu, yace ya nemi ra'ayin dattijan jam'iyyar irinsu tsohon shugaban kasa John Agyekum Kuffour, da tsohon shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasa Kwadwo Mpiani, kuma dukansu sun nuna cewa gwanda a yi zabe kamar yadda aka saba a dimokradiyance, wato a zabi dan takarar shugaban kasa shi kuma ya zabi mataimakinsa.
Baya ga Mahamudu Bawumia da Alan Kyeremanten, akwai wasu da suka bayyana burinsu na shiga takarar, kamar Ministan gona Dakta Owusu Afriyie, da tsohon sakataren jam'iyyar Kwabena Agyapong, da dan majalisa mai wakiltar mazabar Assin ta tsakiya Kennedy Agyapong, da kuma tsohon Ministan makamashi Boakye Agyarko.
Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako: