Rundunar ‘yan sandan kasar Ghana ta kama mutane uku da aka samu da nakiya, da suka hada da wani da ake kyautata zaton dan kungiyar ISIS ne.
Mataimakin Sifeta janar na ‘yan sanda David Asante Apeatu ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, ana kan bincike domin neman karin haske dangane da lamarin.
Masu sharhi kan lamura sun bayyana bukatar sa ido sosai a kan iyakokin kasar inda ake iya shigar da makamai.
Wadansu da Muryar Amurka tayi hira dasu, sun bayyana cewa rashin daukar kwararan matakai a fannin gwamnati yana kara vusa kasar cikin hadari.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Ridwan Abbas ya aiko
Facebook Forum