Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce sun gano gawawwakin yara ashirin a cikin mutane talatin da hudu da suka rasu a yunkurin ketare hamadar jamhuriyar Nijar, jami’an gwamnatin kasar sun bayyana cewa suna kyautata zaton cewar mutanen da lamarin ya rutsa dasu sun doshi arewa ne da niyyar ketarawa kasar Algeria ko kuma shiga nahiyar Turai.
Ma’aikatar cikin gida ta Nijar ta bayyana cewa an gano gawawwakin ne a ranar laraba ta kafar talabijin din kasar inda ta bayyana cewa tara daga cikin su mata ne, da maza biyar da kuma kananan yara ashirin, kuma duka sun rasu ne a sanadiyyar kishin ruwa bayan da masu safarar mutanen suka watsar da su a tsakiyar hamada.
Kawo yanzu dai ba’a tantance ko ‘yan asalin wacce kasa bane. Kuma kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa ta bayyana cewa yawan tafiye tafiyen zawa Turai daga kasashen dake kudu da hamada da yammacin Afirka da afirka ta tsakiya na ci gaba da karuwa.
Yawan tafiye tafiyen dai nada alaka ne da zauwa neman ayyukan yi, kuma ana yawan ganin irin wadannan masu tafiye tafiye ba tare da kananan yara ba suna dosar wadannan wurare.