Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Spain, ta bayyana cewar zata inganta filin wasanta Santiago Bernabeu. Shugaban kungiyar Florentino Perez, shi ya fadi haka inda yace kungiyar za ta sauya fasalin filin wasan nata ne a karshen kakar wasa na bana.
Shugaban ya kara da cewar, sauya fasalin filin wasan zai lashe zunzurutun kudin da ya kai Yuro miliyan €525m kwatan kwacin dalar Amurka miliyan 560, wanda yayi dai-dai da naira biliyan dari biyu.
Ayukan da za'ayi na gyaran filin sun hada sauya fasalin rufin filin da kuma taswirar cikin filin da ake buga tamola, sai kuma sauya fasalin ginin filin wasan daga waje kafin shiga.
Bayan kammala gyaran filin, kungiyar na sa ran samun karuwar kudaden shiga da adadinsu ya kai dalar Amurka miliyan 168, kimanin Yuro miliyan €150m, kwatan kwacin naira milliyan dari shida, a shekara guda inji Florentino.
Shugaban yace gyaran filin wasan na Santiago Bernabeu, zai sa ya zama cikin filaye mafi girma a fadin duniya.
Facebook Forum