Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya musanta rahotannin da ke cewa filin da benen Ikoyi ya rushe a jihar Legas ba nasa ba ne.
Mai magana da yawun Farfesa Osinbajo Laolu Akande ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
“Bari na fito karara na fada, Farfesa Yemi Osinbajo ba shi ya mallaki wannan fili ba kuma bai taba mallakarsa ba.
“Mataimakin shugaban Najeriya ba shi da wata alaka da wannan fili, kuma ya riga tuntuni ya bayyana kadarorin da ya mallaka a baya.” Akande ya ce cikin sanarwar.
A cewar kakakin nasa, mataimakin shugaban kasar ya mika wannan batu ga lauyoyinsa domin su dauki mataki.
Mataimakin shugaban na Najeriya ya kuma nuna alhininsa game da wannan ibtila'i da ya auku tare da mika sakon ta'aziyyarsa da iyalan wadanda abin ya rutsa da su.
A ranar Litinin wani sabon bene mai hawa 21 da ke titin Gerrard Road a yankin Ikoyi ya rufta inda ya danne dumbin ma’aikatan da ke cikinsa.
Wasu kafafen yada labarai (ban da Muryar Amurka) sun ruwaito cewa filin da benen ya rushe na mataimakin shugaban kasar ne, rahotannin da ya musanta.
Ya zuwa ranar Juma’a hukumomin jihar Legas sun ce adadin mutanen da suka mutum ya kai 40 yayin da ake ci gaba da ayyukan ceto.
An kuma ceto mutum tara da ransu kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta LASEMA a jihar ta Legas ta ce.