Hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA, ta aike da sakon taya murna ga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, wadda ta zamo zakarar gasar Firimiya Lig ta Najeriya ta bana, kuma a shekara ta uku a jere.
A cikin wata wasikar da ya rattabawa hannu da kansa ya kuma aikewa Amaju Pinnick, shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, shugaban FIFA, Sepp Blatter, ya yaba da irin rawar ganin da dukkan ‘yan kungiyar Kano Pillars suka taka wajen samun wannan nasara.
Yace wannan nasarar ba wai ta ‘yan wasa da kuma masu koyar da wasa na Kano pillars ba ce kawai, har ma da shugabanni, da likitoci da kuma dubban magoya bayanta. Yace irin wannan sa hannu daga kowane bangare shi yasa kungiyar ta samu nasarar lashe wannan kambi shekaru uku a jere.
Sepp Blatter yace tamaula tamkar makaranta ce ta koyar da rayuwa, kuma matasa zasu iya cin gajiyar irin wannan koyarwa.
Kano Pillars ta lashe gasar Firimiya Lig ta Najeriya a karo na uku a jere, duk da cewa har yanzu akwai sauran wasa guda da ya rage, a bayan da ta doke kungiyar kwallon kafa ta Nembe City da ci 4 da babu a karshen makon jiya a Kano.