Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da shirye-shiryen ta na fadada gasar cin kofin duniya wanda za’ayi a kasar Qatar a shekarar 2022, daga kasashe 48, inda ta yanke shawara zuwa kasashe 32, saboda matsalolin siyasa da tsare-tsare da suka shafi yin amfani da karin kasashe daga yankin Gulf.
Fatan shugaban FIFA, Gianni Infantino, na fadada gasar wacce za a yi a Gabas ta Tsakiya a karon farko, ya fuskanci koma-baya, saboda matsalolin diplomasiyya da yankin ke fama da shi, da kuma bukatar da hukumar ta FIFA ta gabatar ta neman kasashen da za su karbi bakuncin gasar da su kiyaye hakkokin bila adama da na ma’aikata.
Hakan na nufin cewa ba za a kara adadin kungiyoyin da za su kara a gasar ba, har sai zuwa shekarar 2026, duk da cewa lokacin hukumar FIFA ta amince da karin zuwa kasashe 48 a Amurka, Canada da kuma Mexico.
Wani rahoto da hukumar FIFA ta kammala hadawa ya nuna cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain da Saudi Arabia ba za su iya karbar bakuncin gasar ba, har sai sun mayar da huldar kasuwanci da na tafiye-tafiye da suka yanke da kasar ta Qatar shekaru biyu da suka gabata.
Facebook Forum