'Yan Republican sun samu adadin kujerun da su ke bukatar ci a jiya Talata, a zaben Majalisar Tarayyar Amurka, don yin rinjaye a Majalisar Dattawa.
Kafin nan dai 'yan Demokrat na da kujeru 55 daga cikin jimlar kujeru 100 da ke Majalisar, to amma a yanzu jam'iyar Republican ta ci bakwai daga cikin su, inda ta yi nasara a Arkansas, da Colorado da Iowa, da Montana da North Carolina da South Dakota da kuma West Virginia.
Dama dai a jiya Talatar an yi zaben ne akan sulusi daya na kujerun Majalisar wato kashi daya cikin uku, a ciki har da kujerar Kentucky, wadda shugaban 'yan Republican a Majalisar Dattawa Mitch McConnell dan asalin Kentucky ke kai. Yanzu ya ci wa'adi na shida kenan.
Bugu da kari, jam'iyyar ta Republican ta kara karfin rinjayen da dama ta ke da shi a Majalisar Wakilai, wanda hakan ya ba su cikakken iko a Majalisar Tarayyar Amurka, ana sauran shekaru biyu shugaba Obama ya kammala wa;adin mulkin sa na biyu kuma na karhe.
Ma'aikacin Sashen Hausa na Muryar Amurka Salihu Garba ya tattauna da Lauya Aminu Hassan Gamawa na jami'ar Harvard domin yayi fashin baki akan zaben na rabin wa'adi da aka yi jiya Talata a nan Amurka.