A jiya Asabar ne aka samu fashewar wasu tagwayen bama-bamai a wata kasuwa mai hada-hadar jama’a a arewa maso gabashin Najeriya, wanda yayi sanadiyar rayukan mutane 13 da kuma raunata wasu sama da 50.
Jami’ai a Najeriya sunce wasu mata ‘yan kunar bakin wake ne biyu suka kutsa wani wajen da mutane ke hada-hadar kasuwanci dake garin Biu, kimanin kilomita 185 kudu da Maiduguri, wata tungar Boko Haram.
‘daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ta tayar da bam ne cikin babbar kasuwar Biu, yayin da ta biyun ta tayar da nata a wajen kasuwar, a cewar maigana da yawun ‘yan sandan yankin.
Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya fito ya ‘dauki alhakin harin, amma harin na kama da irin sauran hare-hare da kungiyar Boko Haram ta ke kaiwa, wadanda aka sansu wajen yin amfani da mata da ‘yan mata wajen kai harin kunar bakin wake.
Garin Biu da sauran yankunan jihar Borno, sun sha fama da hare-haren kunar bakin wake shekaru masu yawa, yayin da kungiyar Boko Haram ke kokarin ganin ta kafa ‘daular musulunci a Arewa maso gabashin Najeriya.
Makonni biyu da suka gabata mutane 50 suka rasa rayukansu a dalilin wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin Mubi, mai tazarar kilomita 170 daga gabashin Biu.
Gwamnati ta sha tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa ana dab da kawo karshen Boko Haram, kwatsam kuma sai wasu hare-hare su abku.
Facebook Forum