Firaministan Turkiyya Ahmet Davutoglu yace, kasarsa da ta Iran din za su iya hada kai don don kawo karshen zubar da jinin da ake fama dashi. Ya bayyana haka ne da yake jawabi a taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran jiya Asabar.
Ahmet yace, hadin kai zai taka rawar gani wajen kawo karshen fadace-fadacen addinin da ake fama da su. Mataimakin shugaban kasar Iran Eshagh Jahangiri yace, kasarsa da Turkiyya ba su yarda da ake cewa suna da hannu a fadace-fadacen da ake yi ba.
Duk da wannan zargi, kasashen sun ce zasu hada hannu da Turkiyyar bisa yunkurin ganin an sami zama lafiya a yankunan, wanda hakan shine mafi dacewa da al'ummar kasashen da ake hallakawa.
Turkiyya dai itace babbar mai marawa ‘yan tawaye baya don hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a Syria, su kuma Farisa da Rasha na goyon bayan gwamnatin ta al-Assad.