Yankin gabashin Afrika na fama da matsala ta farin-dango mafi girma a cikin shekaru 25, a cewar hukumar abinci da noma ta Majalisar Dinkin Duniya.
Lamarin shi ne kuma mafi muni da kasar Kenya ta gani cikin shekaru 70.
Wadannan farin masu illa ga tsirrai, sun yi barna a kimanin Larduna 11 cikin 47 a kasar ta Kenya, inda suka lalata filayen noma masu tarin yawa.
Masana sun ce idan ba a dauki matakan da suka dace ba, lamarin zai haddasa babbar barazana ga fannin samar da abinci da rayuwar al’ummar yankin.
Wani manomi a Kenya mai suna Theophilas Kimanzi, yana hasashen ya sami amfanin gona mai kyau, amma sai ya tashi da safe a makon da ya gabata ya tarar da farin sun cinye masa amfanin gonarsa.
Ya ce “sun cinye min masara da koren-wake, har ma sun cinye min kankana, sun kuma cinye abinci da muka tanadarwa dabbobinmu. Yanzu ba mu da wani abun da ya rage illa gwamnati ta kawo mana dauki."
Facebook Forum