DandalinVOA ya samu zantawa da Farfesa Kamilu Sani Fagge, na Jami’ar Bayero dake Kano, mun tattauna dangane da dabi'un Majalisun Datijjai da ta Wakilai, da yadda suka harzuko wa Shugaba Buhari a yayin da yake gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.
Tambayar da mukayi mishi itace, ko hakan zai yi tasiri ga tunanin matasa akan tsarin demokaradiyyar Najeriya? domin kuwa sune masu yin doka da oda, sai gashi basu girmama ofishin shugaban kasa ba, ballantana ofisoshinsu.
Farfesa Kamilu ya ce, wannan dabi’ar tasu, bata nuna alkhairi tare da nuna wa matasa cewar siyasar duk hatsaniya ce, sannan idan mutum na neman wani abu na son zuciya, akwai hanyoyi marasa kyau da zasu iya.
Ko da yake, ya ce matasa a baya sun bada gudunmuwa na azo a gani, alal misali lokacin da aka yi yakin basasa, matasa ne suka kwato wa kasar 'yanci tare da tafiyar da harkokin cigaban kasa.
Ya kara da cewa tabbatar da cigaba, ba’a shekaru suke ba, illa akan yadda matasa suke da kishin kasar su, tare da dauke kai daga tunanin cika buri na tara dukiya da kauracewa akidar da ya tsaya a kai har aka zabe shi.
Daga karshe ya bukaci matasa da su daina dora kawunsu akan kwayoyi, kafun su cimma kudurorinsu na biya wa kansu wasu bukatu. Sannan matasa su farga da cewar su 'yan siyasan da suke basu kwayoyi, basa baiwa ‘ya'yansu kwayoyin domin su yi bangar siyasa.
Facebook Forum