Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na MDD akan zargin sayar da bakin haure a Libya


Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya kira taron na Majalisar Dinkin Duniya, MDD
Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ya kira taron na Majalisar Dinkin Duniya, MDD

Kwanan nan kafar yada labarai ta CNN ta fitar da rahoton binciken da tayi a Libya inda masu safarar bakin haure suke sayar dasu a Libya tamkar bayi har ma an nuna wani dan Najeriya da aka sayar dashi akan kudi dalar Amurka 400

Kasar Faransa na bukatar a yi wani taron gaggawa na Kwamitin Sulhu na MDD, don tattaunawa kan zargin sayar da wasu bakin haure ‘yan Afirka a matsayin bayi.

Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana hoton bidiyon al’amarin da gidan talabijin ta CNN ta nuna a makon jiya da “abin fallasa,” wanda kuma “ba za a lamunta da shi ba.”

“Wannan babban laifi ne ga dan’adam,” a cewar Macron bayan ganawarsa da Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Alpha Conde. Ya kara da cewa, “Ina fatan za mu kara azama a yaki da masu safarar mutane wadanda ke aikata wannan danyen aikin, tare kuma da hada kai da dukkannin kasashen da abin ya shafa don wargaza su.”

Kafar ta CNN ta nuna hotunan bidiyon da ke nuna yadda ake cinikin wasu bakaken fata maza akan dala $400 kowanne, wadanda za a rika kai su gona su na aiki. Vidiyon ya janyo bacin rai a sassan duniya kama daga Turai zuwa Afirka.

Mai yiwuwa a yi taron na MDD a makon gobe, a cewar wani jami’in diflomasiyyar Faransa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG