A jiya ne kamfanin Facebook ya sanar da cewar sabon tsarin bayanan sirri, da gwamnatin Amurka ke bukatar ya fara amfani da shi, zai takaita kudaden shiga da kamfanin ke samu.
Kana sabuwar dokar zata sa kamfanin ya dinga kashe makudan kudade wajen aiwatar da sabon tsarin. Kamfanin ya hango wadansu daga cikin matsaloli da zai iya shiga na kudi, tun bayan hukuncin wata kotu da ta umurci kamfanin da ya biya tarar dala biliyan $5B.
Kamfanin da ke mallakar manhajojin WhatsApp da Instagram, ya samu raguwar kudin shiga na hannun jarin shi da kashi 1%, duk dai da cewar kamfanin ya samu kudin shiga a shekarar da ta gabata.
A jiya dai shugaban asusun kamfanin Dave Wehner, ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewar, aiwatar da wannan sabuwar dokar na bukatar saka makudan kudade, musamman ga ma’aikata da na’urorin masu fasahar zamani.
Ya tabbatar da cewar kudaden shiga da suke samu za su ragu matuka. Kamfanin dai ya ruwaito cewar yana da mutane masu ziyar tar shafin a duk wata da suka kai mutane biliyan 2.7, a duk rana kuwa sun kai mutane biliyan 2.1.
Facebook Forum