Shugaban sashen yada labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a yau Juma’a.
“A kokarin da su ke yi na tsaftace Najeriya daga damfarar intanet da sauran nau’ukan zamba, jami’an hukumar EFCC, sun kama ‘yan China 4 da wasu ‘yan Najeriya 101 a wani ginin kasuwanci da ke yankin Gudu na birnin Abuja,” a cewar hukumar EFCC.
Ya kara da cewa an kama wadanda ake tuhumar ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairun da muke ciki, inda yace sun hada da maza 67, ciki har da ‘yan Chinar, da kuma mata 38.
Dandalin Mu Tattauna