Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ebola Ta Kashe Mutum na Farko A Mali.


Shugaba Barack Obama yake taya Nurse Nina Phem murnar ta warke daga cutar Ebola.
Shugaba Barack Obama yake taya Nurse Nina Phem murnar ta warke daga cutar Ebola.

A Mali jami’an kiwon lafiya a kasar sun ce wata yarinya ‘yar shekaru biyu da haifuwa wacce bata juma da komawa kasar daga Guinea ta mutu sakamakon kamuwa d a cutar Ebola.

Mutuwar ‘yar yarinyar jiya jumma’a, shine karo na farko da aka tabbatar da wani ko wata Bil’Adama a kasar ta rasa ranta sakamkon kamuwa da cutar.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya tace yarinyar da iyayenta ko dangi sunyi cudanya da mutane masu yawa yayinda suke balaguro cikin motar safa cikin kasar, daga nan tayi gargadin cewa mutane da yawa suna cikin hadarin kamuwa da cutar Ebola.

Kafofin difilomasiyya sun bayyana damuwar cewa Mali bata da shirin tunkarar cutar Ebola. Mali tana cikin kasashe mafiya talauci a duniya.

Annobar tafi karfi ne a kasashe uku a suke yammacin Afirka, Guinea, Laberiya, da Saliyo. Cutar ta kashe mutane dubu hudu da dari tara. Haka kuma an sami bazuwar cutar jifa jifa a turai da kuma Amurka.

Hukumar kiwon lafiya ta duniyar tace tana shirin samar da dubun dubatan rigakafin kamuwa da cutar ta Ebola a zangon farko na shekara mai zuwa.

Shugabannin kungiyar tarayyar turai sun fada jiya jumma’a cewa sun tanadi dala milyan dubu daya da milyan 25 domin taimakwa a yaki cutar Ebola a yammacin Afirka.

Nurse Nurse biyu da suka kamu da cutar yayinda suke jinyar dan laberiyan nan a wani asibiti dake birnin Dallas yanzu sun warke.

Ahalinda ake ciki kuma, wani sabon mutum da ya kamu da cutar ya tilas hukumomi a New York daukar matakar killace mutane a ciki da kewayen birnin. An tabbatar ranar Alhamis cewa Dr. Craig Spencer ya harbu da cutar bayan da yayi aikin jinyar wadanda suke fama da cutar a kasar Guinea.

A ranar jumma’a gwamnan jihar New York Andrew Coumo da takwaran aikinsa na jihar New Jersey Chris Christie, sun duk wani matafiyi da yayi cudanya da wadanda suka kamu da cutar zasu tilas a killace su na tsawon mako uku.

XS
SM
MD
LG