An sami sama da mutane dubu biyu dauke da kwayar cutar Ebola a Jamhuriyar Damokaradiyar Kwango,bisa ga cewar ma’aikatar lafiya ta kasar,Inda mutane dubu daya da dari uku da arba’in da shida suka mutu, Wanda da ya kasance asarar rayuka na biyu da aka yi mafi girma a tarihi ta dalilin cutar Ebola.
Ranar Litinin ma’aikatar lafiya tace mutane dari biyar da talatin da tara sun yi jinyar cutar sun kuma warke.
Ma’aikatar lafiyar kasar tace ingancin tsaro da ake samu da kuma dakile rayuwarshi ya taimaka.
A halin da ake ciki kuma, kungiyoyin agajin kasa da kasa ta Red Cross da Red Crescent sun ce akwai bukatar sake lale wajen tunkarar cutar bisa la’akari da yadda take kara raduwa.
Facebook Forum