Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Shawo Kan Cutar Ebola Nan Da Makwanni Masu Zuwa - Kwararru


Wani mutum yana wanke hannuwansa a wani mataki na kaucewa kamuwa da cutar Ebola a Congo
Wani mutum yana wanke hannuwansa a wani mataki na kaucewa kamuwa da cutar Ebola a Congo

Kwararru daga hukumar lafiya ta duniya WHO da takwarorinsu na kungiyar likitocin kasa da kasa, sun ce ana gab da shawo kan yaduwar cutar Ebola.

Nan da makwanni masu zuwa, ana sa ran za a dakile sabuwar barkewar cutar Ebola da ta auku, a cewar kwararrun hukumar Lafiya ta Duniya WHO da kuma na kungiyar likitocin kasa da kasa na Medicine San Frontiers.

Sai dai a wata hira da kwararrun suka yi da Muryar Amurka a wannan makon, sun ce, duk da haka, akwai sauran jan aiki a gaba, yayin da daruruwan ma’aikatan kiwon lafiya na gida da waje ke kokarin yaki da cutar ta Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Amma wata alama da ke nuna haske kan lamarin a cewar Dr. Hilde De Clerck, jami'ar lafiya daga cikin hukumomin, ita ce, an gano asalin wuraren da barkewar cutar ta samo asali a kasar ta Congo.

A baya dai, an yi fargabar yaduwar cutar zuwa sassan yammacin Afirka, kamar yadda aka gani a tsakanin shekarun 2014 da 16, inda mutane sama da mutane dubu 11 suka mutu a kasashen Guinea, Liberia, Saliyo, wanda shi ne lamari mafi muni da mutane suka halaka sanadiyar cutar tun da aka gano ta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG