Masana binciken sararrin samaniya sun tabbatar da cewar a wannan duniyar mutane basa iya ganin sauran duniyoyi da ake dasu a sararrin samaniya. Hukumar kula da sararrin samaniya ta Amurka NASA, tace a wannan watan na Yuni mutane zasu ga abun ban-al’ajabi.
Domin kuwa daya daga cikin duniyoyi da ake dasu ta Jupiter zata bayyana da girmanta kuma cikin haske, itace kuma duniyar da tafi girma, wanda idan Allah ya kai rai ranar 10 ga wannan watan, zata bayyana a baki dayan daren ranar, mutane zasu iya ganinta da idon su.
Zata bayyana kusa-kusa, wanda mutane zasu iya amfani da na’urar Telescope don ganin wasu taurari hudu da suke tare da ita, mutane ma na iya ganin kalan jikinta.
Wannan yana faruwa a duk shekara, lokacin da duniyar Jupiter ke ratsa tsakanin duniyar Rana da ta Wata, wanda har zuwa karshen watan za a ga wata ya kasance cikin haske.
Facebook Forum