WASHINGTON D.C. —
Amurka ta ayyana tsare shugabannin fararen hula da sojojin Myanmar suka yi a matsayin juyin mulki, lamarin da ya sa ta ce ta fara yin nazari kan tallafin da take ba kasar wacce ake kira Burma a hukumance.
Hakan na faruwa kuma, yayin da Amurkan ta yi Allah wadai da hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara uku da rabi da wata kotu a Rasha ta yankewa shugaban ‘yan adawar kasar Alexie Navalny.
Yau kan wadannan batutuwan shirin na Duniya Amurka na wannan mako zai mayar da hankali akai tare da Mahmud Lalo.